(ABNA24.com) Gwamnatin tarayar Najeriya ta sami umurnin kotu na haramta harka islamiya ta Najeriya wacce aka fi saninta da “The Islamic Movement In Nigeria” ko IMN.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta sami labarin cewa gwamnati ta dauki wannan matakin ne bayan da shugaban kasa yagana da manya-manyan shuwagabannin hukumomin tsaron kasar.
Labarin ya kara da cewa a jiya jumma’a ce dai gwamnatin ta sami wannan umurnin daga hannun mai shari’a Nkeonye Maha na wata babbar kotu a Abuja.
Umurnin kotun ya na cewa “ Daga yanzu babu wani mutum ko gungun mutane da suke da damar hulda da kungiyar ta yan shi’ar, hulda ta ko wacce iri ce”.
Jaridar ta kara da cewa “domin kammala aikin wannan umurnin, kotun ta bukaci babban jami’I ma’aikatar shariya ta kasa, wato antony janar na kasa, ya shelanta wannan umurnin a cikin manya-manyan jaridun kasar guda biyu. Kafin jaridar Premiumtimes dai, jaridar Punch ce ta fara buga labarin.
Zangar-Zanagar yayan wannan Harka dai tana zama ta tashin hankali, wanda yake kai ga rasa rayuka a cikin yan makonnin da suka gabata, inji jaridar.
/129
29 Yuli 2019 - 03:44
Lambar labari: 965471
Gwamnatin tarayar Najeriya ta sami umurnin kotu na haramta harka islamiya ta Najeriya wacce aka fi saninta da “The Islamic Movement In Nigeria” ko IMN.